Labarai
Ƴan Maulidi 150 sun ɓace bayan da jirgin ruwan da su ke ciki ya kife a jihar Neja


Advertisment
Masu bikin Maulidi 150 ne rahotanni suka bayyana cewa sun bace a yayin da jirgin ruwa, mai dauke da mutane 300 ya nitse a garin Gbajibo na karamar hukumar Mokwa a jihar Niger.
Daily Trust ta rawaito cewa wadanda lamarin ya shafa wadanda dayawan su mata ne da kananan yara, sun bar garin Gbajibo ne don zuwa bikin Maulidi a yayin da jirgin ya nutse da su a tsakiyar ruwa a jiya Talata.
Majiyoyi daga garin, sun ce matuka jirgin ruwa dake garin sun fara ceto wasu mutanen da ran su.
An shaidawa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da karfe 8:30 na dare.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Niger, Alhaji Abdullahi Baba Arah ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai yi karin bayani kan asarar rai ba.