Labarai

Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

Advertisment

Kano – Rahotannin da Legit.ng ta fara tattarowa shine na fara shagalin bikin da daya tilo na shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar sarkin Bichi, Alhaji Nasir Bayero.
Kamar yadda shafin @insidearewa ya wallafa a daren ranar Juma’a, an ga hotunan amarya Zarah Bayero tare da angonta Yusuf yayin da ake gasar kwallon Polon bikinsu.
Wannan alama ce ta yadda aka fara shagalin bikin a ranar Juma’a duk da za a yi asalin daurin auren a farkon watan Augusta.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Inside Arewa Media (@insidearewa)

Advertisment


 
An kai lefen Zarah Bayero a watan Yuli
Har ila yau, duk a cikin watan ne mata suka kai akwatunan aure dankare da kaya na lefen gimbiya Zarah Bayero.
Kamar yadda aka tattaro, biyu daga cikin akwatunan na dankare da zinari da lu’u-lu’u da kuma tsabar kudi.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Inside Arewa Media (@insidearewa)

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button