Labarai

Ƴan sanda sun cafke matashin da yayi garkuwa da yar makocinsa ƴar watanni 18 a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna Zakariyya Muhammad, da ake zargi da laifin yin garkuwa da karamar yarinya mai shekaru biyu da rabi.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, tun a Ranar 4 ga watan Yuli 2024, rundunar ta samu Korafi daga wani Mazaunin unguwar Sabuwar Gandu Kwarin Barka, cewar wani ya Kira wayar sa inda ya shaida masa cewar ya Yi garkuwa da Yarsa mai suna Amina , har aka nemi a biya shi kudin fansa naira miliyan biyu Kafin ya sake ta.

Ƴan sanda sun cafke matashin da yayi garkuwa da yar makocinsa ƴar watanni 18 a Kano
Ƴan sanda sun cafke matashin da yayi garkuwa da yar makocinsa ƴar watanni 18 a Kano
Hoto/facebook

Bayan samun korafin ne Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya tayar da dakarun yan sanda , ma Su yaki da garkuwa da mutane, karkashin jagorancin SP Aliyu Muhammad Auwal, tare da ba Su umarnin kubutar da yarinyar cikin a wanni 24, da kuma Kama Wadanda ake zargin.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya Kara da cewa, an Yi nasarar Kama Wanda ake zargin Zakariya Muhammad , a ranar 5 ga watan Yuni 2024, inda ya tabbatar da cewa lr shi ne ya Yi garkuwa da yarinyar sannan ya nemi kudin fansa.

Rahotanni na cewa tuni aka kubutar da yarinyar kuma likitoci sun tabbatar da cewar Kalau ta ke.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Kano, ya ce an dawo da batun Babban sashin binciken manyan laifuka dake Bomapai, bangaren da ya shafi garkuwa da mutane , kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Rundunar ta ja hankalin iyaye Su dinga kula da yayansu, tare da Jan kunnen matasa cewar wannan ba abin Yi ba ne , kuma ba Sana’a ba ce, musamman a jahar Kano domun ma Su yunkurin aikata ba Su da wajen buya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button