Dakarun Nijeriya sun kuma kashe wani kasurgumin dan fashin daji a Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kashe kasurgumin dan fashin dajin nan, Kachalla Makore da mayakansa da dama a yankin Magami na karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
TheCable ta rawaito cewa mai sharhin nan kan lamuran tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin sun kai farmakin ne a ranar 23 ga watan Satumba.
Bayanan da mai sharhin ya wallafa, ya ce an kashe Makore da mayakansa ne a hanyarsu ta dakko gawar Sani Black wani kasurgumin dan fashin daji.
Sojoji ne suka kashe Black da safiyar ranar.
“Rahotanni sun bayyana cewa, Kachalla Makore da mayakan sa suna kan hanyar su ta dakko gawar Kachalla Sani Blacl da aka kashe a Dan Sadau dake karamar hukumar Maru”, inji Makama.
” An kashe Sani Black a Magama Mai Rake inda ‘yan fashin daji ke ayyukan su.