Kantomomi, Malamai, da masu riƙe da masarautun gargajiya na Kano ta tsakiya sun yi mubaya’a ga Sarkin Kano Sanusi II


Shugabannin riƙo na ƙanananan hukumomi 15 na Kano ta tsakiya, malamai da dukkanin masu riƙe da masarautun gargajiyar yankin, sun yi mubaya’a ga Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, tare da nuna goyon bayan su a gareshi.
Shugabannin riƙon na ƙananan hukumomin, da hakimai, da Malamai, da kuma Dagatai, da masu unguwanni, na Kano ta tsakiya, sun yi mubaya’ar ne yayin da suka ziyar ci fadar mai martaba sarkin Kano na 16, Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, ranar Asabar a fadar sa.
Da yake jawabi ga Dala FM Kano, jim kaɗan da yin mubaya’ar, shugaban ƙungiyar shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin Kano 44, kuma shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Abdullahi Ibrahim Bashir, (Mai Kano) ya ce sun yi mubaya’ar ne bisa yadda mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi, yake da kishi da son ci gaban al’umma.
A nasa jawabin mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, ya hori, shugabannin ƙananan hukumomin na Kano ta tsakiya, Malamai, da Hakimai, da Dagatai, da kuma masu unguwannin, da su mayar a hankali wajen samar da ci gaban al’umma.
Wannan dai na zuwa ne bayan da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya karɓi takardar kama aiki a ranar Juma’a 24 ga watan mayun 2024, bayan da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a dokar masarautun da majalisar dokokin jihar suka yi wa kwaskwarima, wadda ta rushe sarakuna biyar a jihar Kano.
Tsohuwar gwamnatin Ganduje ce dai ta samar da dokar kafa masarautun jihar Kano biyar a shekarar 2019, wanda yanzu haka ta zama tarihi bayan da majalisar dokokin jihar ta yi mata kwaskwarima.
– Dala FM