Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Roki Yan Kwadago NLC Da Su Jingine Aniyarsu Ta Tafiya Yajin Aikin Gama Gari A Ranar Litinin

Yan kwadagon sun fusata ne akan tayin da gwamnati tarayya tayi musu na naira dubu 60 a matsayin mafi kankantar albashin ma’aikata.

Ministan yada labarai na kasa Mohammed Idiris shine yayi wannan rokon a wata takarda da maikatarsa ta fitar mai dauke da sa hannunsa a babban birnin tarayya Abuja.

Ministan yace ya kamata yan kungiyar kwadagon su Fifita bukatun mafiya yawan yan Najeriya sama da nasu bukatun su janye aniyarsu ta tafiya yajin aikin. Wannan nazuwa ne kasa da awanni 6 bayan da yan kwadagon ta bakin shugabnta Joe Ajaero ya tabbatar dacewa zasu tsunduma yajin aikin.

Yace zasu tafi yajin aikin ne dan jan kunne ga gwamnatin tarayya sakamakon yadda zanga zangar da sukayi ta ranar 13 ga Watan Mayu batayi tasiri ba.

Rahmatv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button