Labarai
Kotun Kasar Ingila Ta Daure Shahararren Dan Kasuwar Mai Na Najeriya, Rahamaniyya Oil
Advertisment
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Kotun kasar Ingila ta daure shugaban kamfanin mai na Rahamaniyya Oil, Abdulrahman Bashir tsawon watanni 10.
Kotun ta dauren shine saboda wani cinikin mai da aka yi tsakaninsa da kamfanin Sahara Energy Resource Limited wanda an kawo masa man amma bai biya cikakkun kudin man ba. Mun tattaro muku Labarin daga Rahoton Premium times yanda Rahamaniyya ya bisa wani kaso na kudin amma bai biya sauran ba.
Kamfanin da ya kawo masa man ya nemi su yi sulhu inda aka zauna aka yi zaman tattaunawa. Ya sake biyan wani kaso na kudin amma ba duka ba.
Advertisment
Mai shari’a, Butcher ya bayyana cewa za’a iya ragewa Rahamaniyya yawan watannin zuwa watanni 6 idan ya cika alkawarin da ya dauka.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com