Janar Buratai ya kai ziyara garin Kankara
Babban hafsan sojan ƙasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya isa garin Kankara inda aka sace ɗalibaida dama a makarantar sakandare.
Gwamnatin Katsina ta ce ɗalibai 333 suka ɓata da ba a gani ba a makarantar.
Bayanai sun ce Janar Buratai ya gana da rundunar soji da ta kaddamar da binciken gano ɗaliban da aka sace a ranar Juma’a.
Sannan ya kuma gana da ɗaliban da suka samu hanyar tsira daga daji suka dawo gida.
Babban Hafsan sojan na Najeriya ya tafi Kankara ne tare da tawagar gwamnatin Tarayya da ta ƙunshi ministan tsaro Janar Salihi Magashi mai ritaya da kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya shaidawa BBC cewa yara da dama sun gudo tare da cewa 10 ne kawai suka rage hannun ƴan bindiga.
Ya kuma ce jami’an tsaro sun yi wa yankin Kankara ƙawanya da suke tunanin ƴan bindigar na garkuwa da yaran da suka sace.