Ka da Ka yi Tunanin Aure sai Ka Ajiye N50m,’ ‘Yar Tiktok ta ba Maza Shawara
Wata shahararriyar ‘yar tiktok, Sarah Idaji Ojone ta shawarci maza su daina dauko batun aure idan sun san asusunsu bai cika taf da kudi ba
An jiyo ‘yar tiktok din da aka fi sani da Saida BOJ ta cikin wani shirin ‘Blessing CEO podcast’ tana cewa akalla kowane namiji na bukatar ya ajiye N50m kafin ya kinkimo batun aure.
Meyasa ake son auren namiji da kudi?
Saida BOJ dai ta kafe a kan batun da ta yi na cewa dole sai namiji yana da kudi maganar aure za ta kankama.
Ta zayyano dalilai da dama da yasa take ganin ana bukatar makudan kudin idan har da gaske aure mutum zai yi, kamar yadda Intel Region ta wallafa.
Daga dalilanta, ‘yar tiktok din na ganin dawainiyar yaran da ake sa ran za a haifa, da ita kanta kulawa da matar za su ci kudi ba kadan ba, jaridar legit na ruwaito
Ta ce duk da namiji zai iya yin dace ya samu mace mai fahimtar kowane hali da yake ciki, amma fa ta ce sam bata ba mata shawara su zama masu fahimtar.