Labarai

Da Duminsa: Kasar Ingila na duba yiyuwar kakabawa Najeriya takunkumi saboda zargin take hakkin masu zanga-zangar SARS

 
 
Majalisar kasar Ingila ta tabbatar da karbar korafi kan sakawa gwamnatin Najeriya takunkumi bisa zargin take hakkin bil’adama.
 
Wannan jawabi yana kan shafin yanar gizo na majalisar ne inda ta yi zargin take hakkin masu zanga-zangar SARS dake nuna adawa da cin zalin ‘yansanda.
 
shafin Hutudole na ruwaito kiran kakabawa Najeriya takunkumin ya samu saka ha nun sama da mutane 150,000, kuma majalisar kasar ta bayyana cewa nan gaba kadan zata tafka muhawara akan bukatar.
 
Korafin na neman a kalabawa duk wanda ke da hannu a cin zarafin masu zanga-zangar SARS takunkumi.
 Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button