Labarai

Inda Ranka : Amarya ya gutsurewa angonta al’ura a jihar Kaduna

Rahotanni Daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wata sabuwar Amarya mai suna Habiba ta gutsurewa Angon ta mai suna Salisu Idris Azzakari lokacin yana bacci.

Amaryar ta gutsurewa Angon nata Azzakari, mai kimanin shekaru 40 a sanyin subahi lokacin yana huce gajiya.

Bakin labarin ya faru a karamar hukumar Kudan ta Jihar Kaduna a ranar 26 ga watan Mayun daya gabata.

Salisu Idris ya ce ya kasa gane dalilin ta na yin haka saboda Auren soyayya suka yi watanni hudu da suka gabata, babu gaira babu dalili na dawo daga Masallacin Sallar subahi Ina kwance kawai ta Haye mun ruwanci da kakkaifar wuka ta hari Azzakari na saura kadan ta gutsure ta duka sai da makota suka kawo mun dauki; inji shi

Da farko an fara garzayawa da Salisu Idris, zuwa Asibiti dake Kudan daga nan aka mayar da shi babban Asibitin Karamar hukumar Makarfi, sai dai yanzu matsalar ta Sake Kazanta har an wuce da shi babban Asibitin Shika.

Zuwa yanzu jami’an Yan sanda sun yi nasarar kamata suna gudanar da bincike da zarar an kammala za a mikata gaban kuliya.

Dimokuradiyya TvMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button