Labarai

‘Yan bindiga sun hallaka mutane 40 a wani ƙazamin hari da sun ka kai a plateau

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ƴan bindiga sun kai hari kauyen Zurak da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase a jihar Plateau, inda suka kashe mutane sama da 40 ciki har da ƴan banga.

A cewar mazauna yankin, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5: na yammacin jiya Litinin, lokacin da mutane ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Mazauna yankin sun ce amma ba su iya kai rahoton faruwar lamarin ba saboda rashin kyawun hanyar sadarwa a yankin.

A cewar Sahpi’i Sambo, shugaban matasa a yankin, wanda shi ma ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin, ƴan bindigar sun isa garin ne a kan babura goyon biyu-biyu– dauke da manyan makamai kuma suka fara harbe-harbe.

Ya ce “Fiye da mutane 40 ne suka mutu yayin da da dama suka jikkata. Mazauna kauyen sun gudu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da su domin neman mafaka. Har ya zuwa jiya jami’an tsaro ba su isa wurin ba,” in ji Sambo.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayar da wakilin Daily Trust ya yi ba har ya zuwa lokacin hada rahoton.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button