Labarai

Dr. Sheriff Almuhajir yayi tsokaci akan zuwan Dr. Zakir Naik Sokoto

Advertisment

Dr. Sheriff Almuhajir yayi wannan tsokaci na shafinsa na sada zumunta a yau akan gayyato dr.zakir naik zuwa birnin jihar Sakkwato inda maganar tashi ta kawo cece kuce a karkashin martani inda nan take mutane sunkayi martani sosai akan wamnan magarsa.

Yayi rubutun ne jim kadan amma mutane da yawa sunyi martani irin Dr. Sheriff Almuhajir kamar shi kuma musulmi amma yayi irin wannan magana ga abinda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Dr. Sheriff Almuhajir yayi tsokaci akan zuwan Dr. Zakir Naik Sokoto
Dr. Sheriff Almuhajir yayi tsokaci akan zuwan Dr. Zakir Naik Sokoto

Tunda na ga labarin zuwan Sheikh Zakir Naik Sokoto na ke tamabaya a zuciya ta!!!

Wai shin Professor Mansur Sokoto ya bar Sokoto ne da har mutanen Sokoto za su kashe makudan kudade su kawo Zakir Naik ko dai wasu sun fara Kristancewa ne za’a yi debate din dawo da su Musulumci? Ni bance Zakir Naik ba shi da ilimi ba, amma wallahi, thumma tallahi, thumma qasman billahi bai kai Farfesa Sokoto zunzurutun ilimin fiqhun addini ba, sai dai idan Musulumtar da maguzawa za’ayi to wannan yayi idan suna jin turanci.

Advertisment

Amma fa wannan ra’ayi na ne na kashin kai na.”

Mutane sunyi martani sosai a karkashin sharhi.

@fatima kaita ga abinda ta rubuta:

Kamar fa kaine da kake ganin Murja na daidai kuma tanada abinda zata amfani jama’a dashi. To haka shima Prof yake gani a wurin Zakir.

@Abdullahi lawan kolo Geidam cewa yake :

Dr ai fanninsu ya banbanta dr zakir malamin comparative nea yayinda prof kuma malamin fiqh nea,kowane abu da muhallinsa domin bamuda malamin comparative irin dr zakir kuma haka yasa ya goge wa wadanda ba musulmai bah diyewa shakku wadda har haka yakai ga musulunta wani,kaman yadda ba wadda zai soki zuwan wasu karatun fiqhun addini kasar waje subar maluman gida haka bai kamata ya zamto aibi bah.

@hafsa sani kila abinda take cewa :

Ita rayuwa haka take dama ,yanzu mutane da yawa sunfika ilimi Amman wasu bazasu taba amfani da maganarsu ba Amman kai kanayi sau daya sekaga wani yayi amfani dashi ya kuma shiryu ta sanadinka ,to wani lokacin shuru shiyafi alkhaeri, wani babu wanda yake ganin yana birgeshi se murja kunya kuma wallahi TAs zeyi aiki da maganarta yanaji yana gani fir yaki bin abinda wani babban malamin ze fada .

@abdulkarim muhammad Mustapha cewa yake :

Yanxu Kai ba kudi kuke kashewa wajen kawo mutaneh lokacin maulidi ba. Gaskiya Dr. Watarana kana Saka kanka a cikin abunda Bai shafeka ba.
Dr. Zakir naik ai dole aso zuwansa. Koh cemaka akai da kudinka aka kawosa neh. Kacika yawan shisshigi wlh

@Umar aina cewa yake :

Banbancin shine Influence. Dr. Mansur Sokoto zai iya shekera yana wa’azi ba tare da wani inyamuri yasan anayi ba. Amma shi Zakir shigowarsa kadai wa’azi ne. Amma Dr. Mansur tabbas yanada ilimi.
.

@badamasi jibril cewa yake :

Lokacin da ake gayyato wasu Kodaddun Buzaye daga Moroko suna rabawa muridai Aljanna kana ina? Mai yahana ka magana? Kawai kaje Sokoton kuyi muqabala.

Sannan bakayi maganar nasarar musuluntar da Kiristocin da yayi ba. Ko ba ka farinciki ne?

Ra’ayina na bayyana.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button