Labarai

Buhari Bai Raga Ko Kwabo A Lalitar Gwamnati Ba – Nuhu Ribadu

Advertisment

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaron kasa Nuhu Ribadu ya bayyana

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa halin kuncin da kasar nan ke fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne daga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta gaji baitul malin kasar babu komi a lokacin da ya hau kan karagar mulki watannin baya.

Buhari Bai Raga Ko Kwabo A Lalitar Gwamnati Ba - Nuhu Ribadu
Buhari Bai Raga Ko Kwabo A Lalitar Gwamnati Ba – Nuhu Ribadu

Yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara na hukumar leken asiri ta rundunar tsaro ta 2023 a Abuja a ranar Litinin, Ribadu ya amince da matsananciyar matsalar kudi da ta shafi kasaftar kasafin kudi amma ya tabbatar wa al’ummar kasar cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar ci gaba da samar da ingantaccen tsarin tsaro.

Ina tabbatar muku cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samar da ingantaccen tsarin kula da tsaro don magance kalubalen da ake fuskanta a wannan zamani.

Yana da mahimmanci a gare ku ku sani cewa mun gaji wani yanayi mai wuyar gaske, a zahiri ƙasa mai fatara, babu kuɗi, har ta kai ga cewa duk kuɗin da muke samu a yanzu; muna mayar da abin da aka dauka na bashi

Amma wannan gwamnatin tana yin iya kokarinta don ganin ta cika bukatunmu, musamman sojoji, kuma na yi imanin cewa ku shugabannin za ku iya ba da shaida kan hakan Ribadu yace, majiyarmu ta Liberty tv na ruwaito.

Ya kuma yabawa rundunar sojin kasar bisa jajircewar da suka yi wajen tunkarar kalubalen tsaro da ake fama dashi a ciki da wajen Nijeriya, inda ya yi nuni da cewa an samu sauyi mai kyau da kuma ci gaba.

Da yake kira da hadin kai da goyon bayan hukumomin tsaron kasar, Ribadu ya bayyana kwarin gwiwar cewa idan aka yi azamar shugabanci, al’ummar kasar za su shawo kan matsalolin da suke ciki.

Mu hadu a dunkule, mu ci gaba da tallafa wa dakarun mu da sauran jami’an tsaro da wannan aiki na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button