Labarai

Ya canye kuɗin amininsa naira miliyan ukku, ya hallaka har lahira ya arce da motarsa

Ya yi garkuwa da Abokinsa na kusa Ma aikacin Kedco sannan ya yi masa kisan gilla tare da arcewa da motarsa da wayarsa.

Sadiq Zubairu kenan, dan unguwar Hotoron Arewa, mai shekara 35 a duniya, wanda ya hada baki tare da wasu mutane biyu, inda ya yaudari Abokin sa na kusa, Bello Bukar Adam mazaunin Zawachiki dan shekara 45 a duniya, zuwa gidan sa.

Bayan yaje gidan nasa da motarsa kirar Toyota Corolla, sai kawai suka daure shi, sannan ya rinka dukansa da Muciya, ya rika kuma dora masa dutsen Guga akansa har sai da ya ce ga garinku nanYa canye kuɗin amininsa naira miliyan ukku, ya hallaka har lahira ya arce da motarsa

Ganin haka tasa ya saka gawarsa a cikin bayan motar Marigayin ya tafi can Titin bypass na Hotoro ya jefar da ita.

A sakamakon rahoton rashin ganin Marigayin da yayan sa ya kai ofishin yan sanda hakan tasa aka fara zurfafa bincike, kuma daga bisani aka samu labarin ganin gawar Marigayin ya sheshi a gefen Titi, aka garzaya da ita Asibiti aka tabbatar da mutuwar sa.Ya canye kuɗin amininsa naira miliyan ukku, ya hallaka har lahira ya arce da motarsa

Bayan kama Sadiq Zubairu ya tabbatar da aikata danyen aikin Kuma ya ce abunda ya sashi aikata wannan ta’asa shi ne, ganin ya yaudari Marigayin tare da karbar naira milyan 3 a hannun marigayin da sunan zai samo masa wani aiki, amma da ya fahimci ba zai iya mayar masa da kudin ba, kawai sai ya dauko wadannan mutane yan ina da kisa, suka yi ta’adin tare

Yanzu haka yana komar rundunar yansandan Kano, kamar yadda Abdullahi Haruna Kiyawa Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button