Labarai

Munanan Maza Sun fi Iya ba Mata Cikakkiyar Kulawa cewar Jaruma

Wata jarumar fim ƴar ƙasar Ghana, mai suna Efia Odo, ta bayyana cewa munanan maza sun ƙwarewa wajen ba mata kulawa mai kyau.

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da aka gayyato ta a wani shirin talabijin na Ebitz Show. Shafin dimokuraɗiya ya rahoto.

Munanan Maza Sun fi Iya ba Mata Cikakkiyar Kulawa cewar Jaruma
Munanan Maza Sun fi Iya ba Mata Cikakkiyar Kulawa cewar Jaruma

Ta bayyana cewa a baya tayi soyayya da munanan maza amma ta ƙara da cewa suna da kuɗi saboda ba zai yiwu mutum ya kasance mummuna ba kuma baya da kuɗi.

Efia ta kuma yi bayanin yadda take son a zo mata idan a na son a nemi soyayyar ta.

A kalamanta: Na kusa daina waƙa, ina son na zama shahararren mai ƙira’a Al-qur’ani nan gaba -Ali Jita

“Munanan suna kulawa sosai da mata. Eh tabbar na haɗu da munanan maza a baya kuma mun yi soyayya, sannan suna da kuɗi saboda ba zai yiwu kana mummuna ba kuma ba kada ko sisi.”

“Ina jin cewa idan kana son neman soyayyata, kana buƙatar samu na a wajen da ake tara mutane, kamar wajen cin abinci ko farfajiya. Na tsani wani ya haɗa ni da mutum.”

Haka kuma kana buƙatar ɗaukar hankalina ta sanyar samun haƙora masu kyau, idan haƙorin ka baya da kyau, ba zan iya magana da kai ba. Ba zan iya soyayya da gajerun samari ba saboda gajeruwa ce ni. Sannan sai kana da tarin dukiya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button