Na nemi aiki har guda dubu biyar 5000 bayan kammala digiri na na 2 amma na bige da sayar da dafaffen kwai a kan titi – Inji wani magidanci
Wani matashi mai suna Denis Obili Ogola, ya bada labarin cewa yana da digiri har guda biyu, amma ya kasa samun wani cikakken aiki daya kwakkwara, bayan kammala digiri na biyu a jami’ar da yayi. Shafin Labarunhausa na ruwaito
Aiki dubu biyar ya nema bai samu ba
Ya kara da cewa, sai da ya nemi aiki har sau dubu biyar 5000, amma duk a cikin su bai sami ko guda daya ba.
A halin yanzu, matashin ya koma mai sayar da dafaffen kwai a kan titinan kasar Kenya , inda yake dauka daga wannan titi zuwa wancan.
A cikin dangin su shi kadai ne ya kammala digiri
A cikin dangin su, shi kadai ne ya zama mai digiri, amma hakan bai yi masa wata rana ba. Shine babba a cikin gidan su, kuma duk yan uwan sa da shi suka dogara, amma babu abin da yake iya kaiwa gida saboda halin da yake ciki, duk da kwalayen karatun sa.
Ya kara da cewa,
“tunda na kammala karatu na, na jami’a, ban san me ya sameni ba. Na kammala da sakamako mai kyau, kuma har digiri na biyu ke gareni, amma har yanzu ban sami aiki ba.
” Wannan sana’ar ta tallar kyai a kan titi bata iya bani wata riba ta kuzo mu gani da zan iya kula da koda ma kai na, balle kuma ‘yan uwana”,
Kamar yadda ya fada.
Yana zargin kan sa ko yayi wa Allah wani babban laifi
Wadansu lokuta, har ya kan tambayi kansa cewa ko ya aikata wani kuskure ne, a rayuwar sa wanda Allah yake hukunta shi a kai.
Daga karshe, ya bayyana burin sa na samun aiki mai kyau tare da alkawarin kankame sana’ar kasuwanci, koda ya sami aikin yi mai kyau.