Rarara ya bayyana matsayin A’isha humairah a wajensa
A cikin wani shirin daga kannywood wanda freedom radio kano suke gayyato maza da mata a wannan karo sun samu bakuncin Dauda Kahuta Rarara.
Anyiwa mawakin tambayoyi da dama a can harka wakokinsa da kuma wasu daga cikin abokan hulda musamman ita jaruma A’isha humairah.
Rarara ya bayyana matsayin aisha humairah matsayin ta a wurinsa da kuma abin da ya jawo hankalin ta zuwa ga rarara.
“Matsayin aisha a Wajen rarara itace ta ukku a ofis din mu a muƙamai daga ni sai aminu sai ita Aisha, ba wani abu da ya wuce wannan saboda duk wanda take cikin kamfanina akwai aminci da yarda da mu’amala mai kyau.-inji Rarara
Saboda haka a nan mutane zasu gane cewa maganar soyayya tsakanin aisha da rarara babu wannan zance.
Mutane suna ta fadin kalamai cewa yarinyarsa ce amma shi ya nuna abokiyar aikinsa kuma har mukami gareta a kamfanin sa saboda haka babu maganar soyayya ko maganar aure tsakanin su.