Labarai

Gwamna Radda ya zargi wasu jami’an gwamnati da Jami’an tsaro da taimakawa ‘yan bindiga wajen yaki da matsalar tsaro a Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya zargi wasu jami’an tsaro da jami’an Gwamnati da taimakawa ‘yan bindiga wanda ya ayyana cewar matsalar tsaro ta koma kasuwanci a jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.

A cikin jawaban Radda, ya ce ya zuwa yanzu matsalar tsaro ya zama kamar harkar kasuwanci ce ga masu aikata laifuka, inda ya ce wasu mutanen da ke cikin gwamnati; da wasu mutanen da ke sanye da kayan tsaro, da kuma wasu da ke da alhakin gudanar da ayyukan yau da kullum na jama’arsu suna taka rawar gani wajen ƙin bada gudunmawa gameda kauda matsalar tsaro.

Katsina Reporters na ruwaito ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a gidan talabijin na Channels Television’s a cikin shirin Siyasa A Yau wanda ake gabatarwa.

Gwamna Radda ya ce waɗannan dalilai ne da yawa ya sa ba su da tabbacin su iya kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.

A cewarsa, da yawan wa su mutane ba su da kishin al’ummar su, ya ce abin takaici sun samu wani rahoto a kan ana ɗaukar Matasa da yawa a Arewa ayyukan ta’addanci da Naira 500 kacal.

Gwamnan ya jaddada cewa, batun hasashen da ke tattare da manufar Siyasa a yaƙi da matsalar tsaro a jihar ba gaskiya ba ne.

A shekarun baya-bayan nan, gungun miyagu da aka fi sani da ‘yan bindiga sun sha kai hare-hare a wuraren da akasari a yankunan karkara a yankin Arewa, inda suka yi awon gaba da Mutane da dama tare. da kashe wasunsu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button