AddiniLabarai

Saduwa da Mace yana ƙara mata kwarjini, lafiya da nishadi – Sheikh Abdallah G/kaya

A sheikh Dr. Abdallah gadon kaya yana bayyani a cikin wani karatu na fadin fa’idodi na saduwa da iyali yana karawa mace lafiya, kwarjini da nishadi a cikin wani faifan bidiyo malam yake wannan bayyani yana cewa.

“Saduwa da mace yana ƙara mata kwarjini, lafiya da nishadi, macen da duk ba’a saduwa da ita tana zama a cikin ƙunci a gidanta koda bata faɗa ba, malaman sanin ɗabi’a ɗan adam “psychologists” idan sunka ga mace ta shiga damuwa wace anka kasa gane kanta idan matan aure ce za’a tambaye ta shin mijin ki na sauke miki hakkin saduwa aure?.

Idan tace a’a a nan suke gano zaren ta dalilin da take shiga damuwa shine rashin sauke mata wannan nauyi, bincike ya nuna masana suna fada ko ciwo mace take na zazzaɓi ko wani ciwo idan miji yayi saduwa aure ta, tana samun sauki “relief” ba ga mai ciki, ba wadda take ba mai ciki ba.

Saduwa da mai juna biyu yana da muhimmanci sosai, mijinta y rinƙa amfani da ita.

Muna bayyanin ne akan wasu mazajen idan matar su ta dauki juna biyu su ƙaura ce mata wannan kuskure ne, ba dai-dai bane, ka zalunce ta ka dauki alhakin ta wannan ba dai-dai bane, a wani loton a wani zubin mace mai ciki tafi bukatar namiji fiye da wace bata da ciki, yana sauƙaƙa musu haihuwa, yana kuma rage musu radadin haihuwa, yana ƙara musu karsashi da nishaɗi , Sa’a nan kuma bata cutarwa sai in ya wuce ƙa’ida.

Lafiyar ƴa mace yana da alaƙa da jima’i da kwanciyar aure da ake da mai gidanta ita, wani lokaci mace na ciwon mara bincike ya nuna maniyyi ne yake taruwa yake taruwa wanda ya kamata ya fita sai ya taru sosai, sai ya kunkume ma ta sai ta shiga damuwa wanda shi mijin bai sani ba,wanda kuma ga maganin amma bai yaye mata ba.

Binciken masana ya bayyana cewa a lokacin da mace take al’ada rashin saduwa da ita yakan haifar mata da yawan damuwa saboda ba miji a kusa da ita an hana ayi alaƙar aure da ita.

Annabi (s.a.w) yace idan mace na al’ada koma ayi da ita amma banda saduwar aure, nana A’isha take cewa ina yin al’ada Annabi yasa inyi ƙunzugu in daure inda jinin yake zuba yayi komai dani banda saduwar aure.

Ka duba yadda Annabi ya warware zamantakewa mutane a gidajen su amma ba tare da sun farga sun gane ba.-inji sheikh Dr. Abdallah G/kaya.

Malam ya kara da cewa akwai wata da mai gidanta ya samu matsala na mutuwar tsaye wanda zai samu matsala wanda kwata – kwata zai rasa saduwa da mace ba, ta gayamasa cewa gaskiya bazan iya daukar lokacin da zan yi da kai bansan lokacin da zaka warke ba, babu namiji a kusa dani, mai gida ina gudun in ha’ince ka, inyi lalata da direbobin ka, mai inajin tsoron inyi lalata da yaran gidanka , mai gida ina jin tsoron kar inje makaranta kawaye su hadani da wasu inyi lalata da su, ayi hakuri a sawake min inje inyi aure, yace ba laifi yayi mata ihsani mai hali ne.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button