Kannywood

Kannywood: Tsohon Mijina Ya Hana Ni Sake Yin Aure- Jarumar masana’antar kannywood Hajara Usman


A sati biyu  da ya wuce ranar litanin ne wata bazawara, Hajara Usman ta maka tsohon mijinta a wata kotu da ke zamanta a unguwar Karu da ke Abuja bisa wargaza mata aure da ya yi.

Hajara, da ke zaune a unguwar Asokoro ta fadawa kotu cewa ta auri Adamu Abdullahi a shekakar 2011 kuma aurensu ya mutu a shekarar 2016 kamar yadda shari’a ta tanadar ga ma’auaratan da suka gaza samun cimma zaman lafiya a tsakaninsu.

Ta ci gaba da cewa a lokacin suna zaman aure da tsohon mujin nata, ya gallaza mata ba da hakkinta ba.
Hajara ta fadawa kotu cewa “Asali dai ba soyayya muka yi da tsohon mijina ba, iyayena ne suka aura min shi, kuma bayan mun yi auren ne na fahimci cewar yana da bakar zuciya”.

“A duk lokacin da ya yi fushi, yakan yi mini dukan tsiya. Iyayensa da nawa iyayen sun sha ja masa kunne akan yadda ya ke yi min dukan kawo wuka, amma ya ki ji”.

Hajara ta ce, Abdullahi ya saketa a watan Nuwamban 2016, inda ya gaggauata korata daga gidansa bayan ya furta kalamar saki har sau uku a gareni, wanda hakan ke nuna cewa ya yi min saki uku”.

“Tun bayan sakin da ya yi min na yi iddah ta kamar yadda shari’a ta tanadar, amma sai tsohon mijina ya ci gaba da hana manema na aurena”.

Bayan iddah ta, maza har biyu sun nemi su aure ni, amma da zarar mijina ya samu labari sai ya zo ya lalata lamarin.

A watan Afrilun wannan shekarar ne manemi na na farko ya nemi da ya zo ya kawo kudina, amma sai tsohon mijina ya turo ‘yan daba suka zo suka tarwatsa masu kawo kudin aure.

A karo na biyu kuma shi ne wanda ana shirin bikina da wani kuma na daban bayan ya lalata na farkon. A nan ma dai tsohon mijina da wasu ‘yan banga ya taremu a hanya ya tarwatsa tawagarmu kana ya kamani ya yi min dukan tsiya, ya kuma fada min cewa sai ya yi min lahanin da babu namijin da zai ake cewa yana sona.

Hajara ta yi kira ga kotu da ta tilasta tsohon mjinta da ya fita daga hanyarta ta yadda za ta samu ta yi aure, tunda a karo biyu yana korar mata mazan da suka shirya auaurenta.

Daga:- Alummata

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button