Labarai

Akwai bashin yi wa Shugaba Tinubu biyayya da ɗa’a kan kowane ɗan Najeriya’ – Shettima

Advertisment

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya duƙufa ka’in-da-na’in wajen samar da ayyukan raya ƙasa a dukkan faɗin ƙasar nan.

Da ya ke jawabi yayin da Kungiyar Dattawan Jihar Barno suka kai masa ziyarar Barka da Sallah, bayan kammala azumin Ramadan, Shettima ya yi kira da a ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin Tinubu, domin tsare-tsaren da gwamnatin sa ke ci gaba da yi za su amfani kowa da kowa a ƙasar nan.

A cikin maziyartan har da wasu jiga-jigan APC na jihar Barno da wasu masu ruwa da tsakin faɗa-a-aji.

Shettima ya buga misali da matsalar wutar lantarki a Maiduguri, inda ya ce saboda Tinubu ya nuna damuwa kan lamarin kuma tuni ya bada umarnin warware matsalar wuta a Maiduguri da sauran garuruwan cikin jihar.

“Akwai nauyin bashin yi wa Shugaban Ƙasa biyayya da ɗa’a a kan mu. Kuma wajibi ne mu zama masu bin doka da oda. Tinubu ya kamo bakin zaren, yanzu ƙuƙƙullawa yake yi. Idan aka yi kyakkyawan nazari kan tattalin arzikin mu, za a ga cewa ana samun ci gaba a ɓangarori da dama.” Inji Shettima.

Daga cikin waɗanda suka halarta har da Sanatan Barno ta Tsakiya, Kaka Shehu Lawan da wasu ‘yan majalisa.

Yayin da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Dattawan Jihar Barno, Gambo Gubio, ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, tare da nuna amanna da gaskata Shugaban Ƙasa.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button