Labarai

Bayyanin shugaba Buhari Yayi Game Da Zabukan Da za’a yi Ranar Asabar

Advertisment

Mun ji labarin sakon bayanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a game da zaben gwamnonin jihohi da kuma ‘yan majalisar dokoki na jiha da za ayi Ranar Asabar dinnan mai zuwa a Najeriya.

Shugaban kasa ya bayyana cewa dole jami’an tsaro da hukuma su kyale Najeriya su zabi duk wadanda su ke so. Shugaba Muhammadu Buhari a wannan karo ya sake fadakaar da mutane da su zabi ‘yan takarar kowace Jam’iyya. Buhari yana mai cewa idan jama’a sun amince da ‘yan takarar da su ka fice daga jam’iyyar sa ta APC, su ka koma wasu jam’iyyu, to su zabe su, muddin za su kamanta masu adalci tare da yi masu gaskiya idan har su ka samu mulkin jiha.

 Shugaba Buhari dai ya nuna cewa bai da matsala da duk wadanda su ka tsere daga jam’iyyar APC mai mulki su ka nemi takara a wasu jam’iyyun hamayya. Shugaban kasar yace abin da yake so, shi ne ya ga an yi gaskiya a zaben na 2019. A jawabin na shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa yana takaicin ganin an yi magudi da ha’incin zabe don haka ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu yayi aringizo ko kuma yayi amfani da ‘yan daba wajen tarwatsa zabe. Shugaban kasan yayi wannan magana ne a wani faifen murya wanda ya shigo hannun mu a karshen makon nan. A karshen makon nan da aka shiga ne za ayi zaben Gwamnonin jihohi a fadin Najeriya.

Rahoto:legit.ng

Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button