Labarai
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 15 a Sokoto
An tabbatar da mutuwar mutum 15 sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta faru a wasu ƙananan hukumomi shida a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar wato NEMA inda ta ce sama da mutum 27,000 wannan bala’i ya shafa.
Ƙananan hukumomin da bala’in ya shafa sun haɗa da Goronyo da Rabah da Arewacin Sokoto da Wamakko da Silame da Binji, bbchausa na ruwaito
Rahoton da jaridar ta samu daga hukumar ya nuna cewa mutum 5,254 sun rasa muhallansu inda wasu mutum 12 kuma suka samu raunuka sakamakon rugujewar gine-gine.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com