Labarai

Zanga-zanga ta ɓarke a garin Birci kan yawaitar hare-haren ‘Yanbindiga a sassan Kurfi

Advertisment

Zanga Zanga ta ɓarke a garin Birchi bayan harin da Yan Bindiga suka Kai cikin dare a garin Wurma a karamar hukamar Kurfi

Katsina Post ta samu cewa wannan shine karo na biyar da ‘yanbindigar ke kai hari a garin wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma kona dukiyoyi a garin.

Katsina Post ta samu cewa Ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kurfi, Hon. Zaharaddeen Usman Sani ya gabatar da kuɗirin gaggawa da yake neman Gwamnatin jihar Katsina tayi gaggawar samar da tsaro a garin Wurma da wasu sassan ƙaramar hukumar Kurfi.

Hon. Zaharaddeen ya sheda ma zauren Majalisar cewa tun farkon watan Febareru ‘yanbindiga ke aiwatar da hare-hare da dama a wasu sassan ƙaramar hukumar.

Yace ko a satin da ya gabata sun afka garin Wurma suka kashe mutum 9, da jikkata 15 da yanzu haka ke kwance a asibiti.

Ya tabbatar ma zauren da cewa ko a jiya yan’bindigar sun sake komawa garin inda suka kona asibiti, motoci da kuma dukiyoyin al’umma.

Hon. Zaharaddeen Usman yace ya zama wajibi ɓangaren zartarwa ya ɗauki matakin gaggawa don kare rayuwa da dukiyoyin al’umma.

Shima Ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari, Hon. Mustapha Tukur ya buƙaci yan’majalisar da su shirya gagarumin taron addu’a da fatan Allah yayi maganin ta’addancin da mutanen dake ɗaukar ɗawainiyar su.

 

Bayan sauraren ƙudirorin mataimakin Kakakin majalisar, Hon. Abduljalal Haruna Runka, wanda ya jagoranci zaman, ya umarci akawun majalisar da ya miƙa saƙon ga ɓangaren zartaswa don ɗaukar matakin gaggawa.

-katsina post

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button