Labarai

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 200 a asibitin Gaza

Advertisment

Yakin da Isra’ila ke yi da Falasdinawa a Gaza – wanda ke cikin kwana na 174 – ya kashe akalla mutane 32,490 tare da raunata 74,889, a daidai lokacin da Firaminista Netanyahu ya ce Falasdinawa za su iya “kaucewa” daga mamayar da za a yi a Rafah.

Sojojin Isra’ila sun kashe fiye da Falasɗinawa 200 a wani samame da ta kai Asibitin al-Shifa dake birnin Gaza, a cewar rundunar sojin.

Wata sanarwar rundunar sojin ta ce har yanzu dakarun suna cikin asibitin suna fafatawa.

Ta ƙara da cewa, “An kawar da masu zagon ƙasa kusan 200.”

Rundunar ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kwashe fararen hula da marasa lafiya, da ma’aikatan lafiya zuwa wani bangare na asibitin “wanda sojojin suka shirya kuma suka kafa don ba da damar ci gaba da kula da lafiya.”

Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan asibitin da cibiyar kiwon lafiya mafi girma a Gaza da ke dauke da dubban marasa lafiya da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu, a ranar 18 ga Maris.

– TRT AFRIKA HAUSA

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button