Shin wai masu caccakar shugaba Buhari saboda tantabaru sun ki tashi basu da aikin yi ne? ~ Fadar Shugaban kasa
A ranar tunawa da ‘yan Mazan jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya saki tantabaru a matsayin wata alama ta zaman lafiya.
Saidai sun ki tashi inda yayi ta fama, amma daga baya sun tashi. Wannan lamari ya jawo cece-kuce sosai tsakanin ‘yan Najeriya.
A martani ga wannan lamari, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa dalikin da yasa tantabarun suka ki tashi shine. An ajiye su sun dade a cikin keji kuma sun saba da zaman kejin. Yacs to da aka budesu sun ga abin sabon abu shiyasa basu tashi ba. Yace kuma kusan kowace dabba da aka tsare a waje daya haka takan yi.
Kamar yadda hutudole na ruwaito.Yace amma daga baya duk sun tashi da kadan kadan. Ya kara da cewa shin wai masu caccakar shugaban kasar har suna alakanta hakan da wasu lamura basu da aikin yi ne sai neman laifin shugaban kasarsu?
Yace to su sani shugaba Buhari bashi da lokacinsu, yana can yana kokarin ganin yanda zai inganta ayyukan tattalin arziki, Ilimi, tsaro.