Labarai

Mu Daina Ganin Wannan Fitinar Ta Boko Haram A Matsayin Matsalar Arewa Kaɗai ~ Zulum

a cikin jawabin Gwamna Zulum a jihar Lagos,
Mai Girma Gwamna Babagana umara Zulum ya ce idan jihar ba ta kasance cikin lumana ba, sauran sassan ƙasar ba za su taba zama cikin lumana ba.
Yayin da yake jawabi a wajen taron laccar shekara ta Gani Fawehinmi karo na 17 a Legas, Zulum ya ce kalubalen tsaro a Borno na da haɗari ga kowane bangare na ƙasar kuma dole ne kowa ya taru ya yaƙe shi.
Ni daga jihar Barno nake, kuma da yawa daga cikin ƙungiyar Boko Haram yan Najeriya ne. amma kuma mutane da yawa suna ɗaukar nauyin su a duk faɗin duniya. A cikin kungiyar ta Boko Haram, muna da fararen fata, Asiya, ƴan Afirka,da Kirista da wasu baragubin Musulmi.
“A duk Arewacin Najeriya musamman jihar Borno, wani kwamiti na aiki kan yadda za a sake fasalin tsarin karatun Almajiri. Muna so mu inganta tsarin ilimin boko da na zamani don wadatar da waɗannan yara ilimin boko da na lissafi domin su iya tsayawa da kansu, kuma ba ma goyon bayan barace-barace a kan titi.”
“Dole ne mu daina ganin wannan fitinar a matsayin matsalar Arewa. Nisan da ke tsakanin jihar ta Borno da jihar Legas ya kai kimanin kilomita 1,700, amma fa a kula idan har jihar Borno ba ta kasance cikin lumana ba, sauran bangarorin ƙasar nan ba za su taba yin zaman lafiya ba. Dole ne mu haɗa kai mu yaƙi waɗannan mahara. Mun ga abin da ya faru a Libya, Iraki da sauran ƙasashe. Gina zaman lafiya da haɗin kan jama’a suna da matukar mahimmanci wajen ƙarfafa ƙarfin al’ummominmu.”
“Har sai mun kawar da son zuciya, ƙabilanci da kuma amfani da addini, ba za mu samu daidai a ƙasar nan ba. Tsarin mulki ya bayyana a sarari kan buƙatar zaman lafiya a tsakaninmu baki ɗaya, shi ya sa aka sanya tsarin dabi’ar tarayya a cikin kundin tsarin mulki, amma an ci zarafinsa.“ Inji shi
An yi ta kiraye-kirayen a ƙirƙiro ƴan sandan jihohi don su taimaka game da tsaron cikin gida, amma gwamnan ya ce ba ya goyon bayan wannan ra’ayin, yana mai cewa hakan zai ƙara kawo ruɗani ga tsarin da tuni ya lalace kuma zai raunana haɗin kan ƙasa.
Saboda haɗin kan ƙasa, ba zan ba da shawarar a kirkiro ƴan sandan jihohi ba. Lokaci bai yi ba da za mu samu, amma lokaci ya yi, ra’ayin samun ‘yan sandan jihohi yana da kyau sosai. Wannan shine ra’ayina”. Inji gwamna Zulum
Voice of Borno……

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button