Kannywood

Rundunar yan sanya ta gurfanar da jaruma Amal Umar a kotu

Advertisment

Rundunar ƴan sanda shiyya ta daya Zone One, dake nan jihar Kano, ƙarƙashin AIG Umar Mamman Sanda, sun gurfanar da guda daga cikin ƴan masa’antar shirye fina-finan Hausa ta Kannywood, mai suna Amal Umar, a gaban kotun majistiri mai lamba 24, dake zamanta a unguwar Gyadi-gyadi.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan shiyya ta daya wato Zone One CSP Bashir Muhammad ya fitar, aka aikowa gidan rediyon Dala FM Kano.

An dai gurfanar da Amal Umar ne a gaban kotun bisa zargin ta da yunƙurin bada cin-hancin Naira Dubu Ɗari Biyu da Hamsin, ga ɗan sandan da ke bincike a kan wani laifi da ake zargin da hannun ta wajan aikata wa.

 

Advertisment

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button