Turji ya tilasta mana zuwa Abuja don nemo masa kudi – Zamfarawa
Kasurgumin ‘dan bindigar nan da ya addabi al’ummar Zamfara ta Najeriya, Bello Turji ya tilasta wa magidanta yin balaguro zuwa babban birnin kasar Abuja domin tattaro masa kudaden harajin da ya yanke musu ko kuma ya aika su lahira.
Tuni wannan bawan-Allah ya isa birnin Abuja, yana buga-bugan neman kason da aka yanke masa na Naira dubu 11 domin tsira da ransa da kuma na iyalansa kamar yadda ya shaida mana.
Kuna iya latsa alamar link da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsa da wakilinmu na Abuja Mohammed Sani Abubakar.
Kazalika mutumin ya bayyana cewa, Turji na yin zairga-zirgarsa tare da mukarrabansa cikin tunkaho tsakanin al’umma, inda har yake zuwa Masallacin Jumma’a don yin sallah ba tare da wata farbaga ba.
‘Yan bindiga dai na ci gaba da kaddamar da hare-hare kan al’ummar yankin arewa maso yammacin Najeriya musamman Zamfara da Sokoto da suka fi fama da musibar ‘yan ta’addar.
‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana bacin ransu kan yadda gwamnatin kasar ta gaza tabuka abin kirki wajen shawo kan wannan matsalar tsaron baki-daya.
A baya-bayan nan, ‘yan bindigar sun kona wasu fasinjoji kurmus a cikin motarsu a jihar Sokoto, lamarin da ya girgiza al’ummar Najeriya, yayin da matasan kasar suka shirya gudanar da zanzga-zanga domin aika sako ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.



