Labarai

Isra’ila ta kashe gomman Falasɗinawa a ranar farko ta Azumin Ramadana

An kashe gomman Falasɗinawa an raunata da dama a wani hari da Isra’ila ta kai a Gaza a rana ta farko ta Azumin Ramadana a ranar Litinin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu wato WAFA ya ruwaito.

Rahotanni sun ce jirgin yaƙin Isra’ila ya kashe mutane a dama a unguwannin Zaytoun da Sabra da kuma birnin Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza.

Haka kuma sojojin na Isra’ila sun ƙona wata gona a unguwar Salam wadda ke a birnin Rafah.

 

Wani labari : Isra’ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 67 a kwana guda

 

Akalla Falasdinawa 67 ne Isra’ila ta kashe yayin da wasu 106 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a daidai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza da ta yi wa kawanya, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar a yau Litinin, ranar farko ta watan Ramadana.

Wannan ya jawo adadin Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe ya kai 31,112 tare da raunata 72,760 tun bayan soma wannan yaƙin.

Haka kuma ma’aikatar lafiyar lafiya ta sanar da cewa akwai aƙalla mutum 25 da suka rasu sakamakon ƙishirwa da yunwa.

– TRT Afrika

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button