Labarai

Illolin cire ‘yar-wuya ga lafiyar jarirai

Al’adar cire ‘yar-wuya ga jarirai wato “traditional uvulectomy” a turancin likita, daɗaɗɗiyar al’ada ce a ƙasar Hausa. Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa abin da Bahaushe ke cewa ‘yar-uwa, wacce ke da sifar tsiro ko kuma kan yatsa, a can cikin baki daga sama, wani rumbu ne da ke ɗauke da ƙwayoyin garkuwar jiki domin yaƙar cutuka daban-daban. Sai dai, al’adar Bahaushe ta gudana kan cire ‘yar wuyan ga jarirai tsawon zamani, musamman a ƙasashen Hausa da kuma wasu ƙasashen Afrika. Shafin lafiyar uwar jiki na ruwaito

Malam Bahaushe dai yana ganin cewa ‘yar-wuyan wani tsiro ne da zai iya cutar da jariri yayin shayarwa ko kuma ya kawo ciwon maƙogaro can gaba. Sai dai, wannan al’ada ta yi baram-baram da binciken kiwon lafiya a yau, a maimakon haka ma, cire ‘yar-wuyan na iya jefa lafiyar jariri cikin haɗura kamar haka:

1. Yi wa jariri mummunan miki/rauni a ganɗa.

2. Ciwo tare da kumburi a ganɗa.

3. Ɓallewar jini, musamman ga jariran da kan zo da larurar tsinkewar jini bayan miki.

4. Shigar ƙwayoyin cutuka ta hanyar wuƙa ko askar da aka yi amfani da ita wajen cire ‘yar-wuyan, ko kuma shigar ƙwayoyin cutuka cikin raunin da aka yi bayan cire ‘yar-wuyan.

5. Shigar ƙwayar cuta mai janyo ƙaƙƙamewa ko kakkafewar jiki, wato “tetanus” a turance, saboda haɗarin shigar cutar ta hanyar amfani da aska mai tsatsa.

6. Matsalar shayarwa — saboda raunata hanƙa, jariri kan fuskanci wahalar haɗiyar nono yayin shayarwa.

Daga ƙarshe, likitoci sun tabbatar da cewa barin ‘yar-wuya ba shi da wata matsala ga lafiyar jariri, kuma shi ne ma mafi alfanu ga lafiyar jaririn. Kuma cire ta na iya jefa lafiyar jariri cikin haɗuran da aka ambata a sama.

Shan magungunan Malaria da typhoid ba tareda awun jini ba, ba namu bane sabida wadannan alamomin:

1- Zazzabi
2- Ciwon kai
3- Tashin Zuciya
4- Amai
5- Gudawa
6- Ciwon jiki
7- Atini
8- Dachin Baki
9- Rashin Cin Abinci
10- Rashin Karfin jiki.
11- Kasala
12- Kumburin ciki
12- mutun yaji ya rasa abinda yake masa dadi.

Wadannan abubuwan basu tsaya ga alamomin Malaria da Typhoid su kadai ba suna daya daga cikin alamomin HIV da Ciwon Hanta.

Ina mai baku shawarar ku tabbatar kunyi gwajin jini kafin ku fara shan Magani…

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button