An ga jinjirin watan Ramadana a Saudiyya


Za a soma azumin ne a gobe Litinin, 11 ga watan Maris ɗin 2024, wanda ya zo daidai da 1 ga watan Ramadana shekarar ta 1445 bayan Hijira.Rahotanni daga ƙasar Saudiyya na cewa an ga jinjirin watan Ramadana a ƙasar.
Shafin Haramain Sharifain ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta.
Za a soma azumin ne a gobe Litinin, 11 ga watan Maris ɗin 2024, wanda ya zo daidai da 1 ga watan Ramadana shekarar ta 1445 bayan Hijira.
Tun da farko dai an rinƙa samun cikas wurin ganin watan a sassa daban-daban na Saudiyya sakamakon hazo da kuma ƙura wanda har aka soma cire rai daga ganin watan. Sai dai daga baya an tabbatar da ganin watan a ƙasar.
Dama a kowace shekara ana soma duba watan na Ramadana ne a ranar 29 ga watan Sha’aban, idan an ga watan akan tashi da azumi washe gari, amma idan ba a gani ba, akan cike watan na Sha’aban kwana 30 sai a tashi da azumi ranar ɗaya ga watan Ramadana.
~TRT AFIRKA
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





