Labarai

Yadda dan shekara 50 ya yiwa yara yan shekara 3 zuwa 5 Fyade a jihar Katsina—Rundunar Yan Sanda

Advertisment

“Jami’an Yan Sanda Sun Kama Dan Shekaru 50 Da Laifin Yi Wa Kananan Yara Masu Shekara Uku Zuwa Biyar Fyade A Katsinan Dikko”
Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jajirtaccen kwamishinan yan sanda, Alhaji Sanusi Buba ta yi nasarar damke wani tsoho mai shekaru hamsin da haihuwa dan asalin garin Dauki dake karamar hukumar Batsari, amma yana zaune a cikin garin Katsina a Unguwar Modoji dake cikin garin Katsina, bisa zargin yin lalata da kananan yara masu shekaru ukku da kuma biyar da suke zaune a gida daya a Unguwar Modoji cikin garin Katsinan Dikko.
Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya baje kolinsa ga manema labarai a helkwatar rundunar dake Katsina a ranar Litinin.
A cewar Gambo Isa ya kara da cewa Abdulkadir Abdulkarim ya yi wa yaran fyade a gidansa da suke zaune a gida daya, kuma a cikin binciken ya amsa laifinsa kuma har ya ce yana ba su naira ashirin zuwa talatin da wani abu.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a helkwatar rundunar, wanda ake zargin ya ce muna zaune a gida daya, wanda iyayen yara suka ba shi gidan ya zauna kyauta, kuma ya amsa laifinsa, inda ya ce kaddara ce, saboda ina da mata da yara, amma maza ne. Ana ci gaba da bincike domin maka shi gaban kotu domin yi masa hukuncin daya dace.
Daga: shafin apa hausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button