Dawo da Tallafin Man Fetur shi ne mafita yadda talakawan Nijeriya Za su Samu sauki – Kwankwaso


Dawo da Tallafin Man Fetur shi ne mafita yadda talakawan Nijeriya Za su Samu sauki
Amma bayar da tallafin kuɗi da Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi bashi da Wani Amfani yaudarace tsantsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya amayar da fushinsa.
Babu Abinda ke cikin shirin gwamnatin BOLA TINUBU na rabawa yan NIGERIA tallafin rage raradin cire tallafin man fetur illa DAMFARA
Ya kara da cewa: A irin wannan mayuyacin yanayi babu wata mafuta da wannan tsari zai kawo, idan har gaskiya ne to ba wannan hanya za abi ba wajen rabon tallafin matukar so ake kowanne TALAKA ya samu, duba ka ga yanda mafi rinjayen al ummarmu na AREWA maso YAMMA suke rayuwa, kaso nawa ne suke amfani da asusun banki? Amsa bayyane take yan kalilan ne, Kaga kai tsaye saidai mu kira wannan Abun yaudara da damfara kawai ga Al ummarmu.
Kwankwaso yace: Bari na baka wani misali amatsayina na wanda ya rike chairman na harkokin banki na shekara hudu. Na san Al amura irin wannan da suka shafi kudi da tattalin Arziki,.
Ka gani? Al ummar Arewa Kashi saba in zuwa da biyar 70/75 duk basu da wani Abu Account, ka isa kace wayan nan mutane da suke kada mafi rinjayen kuria a zabe basu da Amfani?
Ya zama wajibi mu wakilan Arewa mu farka domin idan bamu yunkura ba, Za a ci da rabon Al ummarmu kuma sai ALLAH ya kamamu.