Majalisar dinkin duniya ta sanar da tallafin Dala Miliyan 6 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Borno


Ko-odinetan jinkai a Nijeriya na majalisar dinkin duniya, Mohammed Fall, ya sanar da bada tallafin Dala Miliyan 6 daga asusun jinkai na Nijeriya ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.
A ranar 10 ga watan Satumba ne dai, Dam din Alau ya balle inda ya haifar da ambaliyar ruwa wacce ta tafi da dubban gidaje a garin Maiduguri, daily Nigerian Hausa na ruwaito.
Mai magana da yawun majalisar dinkin duniya, Stephane Dujarric, a wani taron manema labarai a birnin New York, ya ce aikin hadin gwiwa tsakamin majalisar dinkin duniya da kungiyoyi masu zaman kansu sun ziyarci birnin Maiduguri a karshen mako.
Dujarric ya ce sun gana da mutanen da abin ya shafa wadanda dayawansu sun rasa gidajen su sakamakon matsalar tsaro.
“Mu da abokan huldar mu muna basu dafaffen abinci, muna samar da abinci ta sama ga wuraren da suke da wahalar shiga.
” Muna kuma basu ruwa da kayan tsafta domin dakatar da barkewar cututtuka.”