Labarai

Mun cafke waɗanda sunka karkatar da buhunan 1238 da za’a kai sansanin ƴan gudun hijira – ƴan sanda

Advertisment

An kama mutane biyar da laifin karkatar da buhunan alkama 1,238 da aka nufi sansanin ‘yan gudun hijira na Kano

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kwato buhunan alkama 1,238 da aka tanadar wa sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Kano.

Rundunar ‘yan sandan ta ce buhunan alkamar sun fito ne daga hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya UNWFP.

A wata sanarwa da kakakin rundunar Muyiwa Adejobi ya fitar ranar Lahadi, ya ce buhunan alkama guda 1,238 ne za a kwashe daga tashar tashar Ibeto ta Fatakwal zuwa Kano, amma aka karkatar da su.

Adejobi ya ce an kama mutanen biyar ne a Fatakwal a ranar 6 ga Fabrairu, 2024 kuma an kwato kayayyakin.

“Buhunan alkama guda 1,840 da za a dauko daga tashar Ibeto Port-Harcourt zuwa sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar Kano, direbobin da aka dorawa alhakin wannan aiki tare da abokan aikinsu ne suka karkatar da su cikin damfara.” Kakakin rundunar ya ce.

“Jami’an sun kama mutane biyar (5) da ake zargi da suka hada da Umar Hashim, Edidiong Umoh, Udah Stanley, Abubakar Jariri da Yunusa Babangida, tare da kwato buhunan alkama guda 1,238 da aka sace tare da babbar mota da wata motar safa da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.

“An mayar da buhunan alkamar da aka kwato ga hukumar samar da abinci ta duniya, kuma ana kokarin kwato buhunan alkama 602 da suka bata tare da kama sauran wadanda ake zargi da aikata laifin.”

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button