Sojojin Kasar Rasha Sun Zagaye Birnin Da Daliban Najeriya Ke Ciki A Ukraine


Kusan dalibai yan asalin Najeriya 370 ne suka maƙale a wani birnin ƙasar Ukraniya da Sojojin Rasha suka zagaye.
Daliban da suka maƙale a cikin na fuskantar barazanar cutarwa kasancewar dakarun Rasha sun kara zafafa kai hare-hare biranen Ukraniya a yaƙin da ya shiga rana ta 7 ranar Laraba.
Sakatare na biyu a ofishin jadancin Ukraniya a Najeriya dake Abuja, Bohdan Soltys shi ne ya faɗi haka yayin fira da Leadership ranar Laraba.
Ya ce ɗaliban Najeriya dake cikin birnin Sumy sun maƙale, kuma babu wata hanyar fita daga birnin saboda sojojin Rasha sun zagaye shi baki ɗaya.
Ya kuma roki gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, musamman hukumomin jin kai su gaggauta yin wani abu domin tseratar da yan Najeriya daga mamayar sojojin Rasha.
Daga Comr Abba Sani Pantami