Labarai
Mun kara farashi ga kwastomomin mu saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasa, Kungiyar Karuwai
Advertisment
Wata kungiyar karuwai da ke Accra, kasar Ghana ta bayar da sanarwa dangane da yadda farashin aikin su ya karu, LIB da labarunhausa na ruwaito.
A cewar kungiyar, tabarbarewar tattalin arziki tare da tsadar man fetur ne yasa wajibi suka kara tsadar aikin na su.
Yanzu haka, wajibi ne kwastoma ya dinga biyan tsakanin $50 zuwa $300, kuma kada ya kuskura ya wuce mintina 15 zuwa 20.
Har ila yau, wajibi ne kwastoma ya lale $300 ya biya idan hara yana da niyyar kwana.
JoyNews ta ruwaito yadda karuwan suka bukaci kwastomomin su akan su kara hakuri dangane da karin farashin.