Labarai

TINUBU Na Tsaka Mai Wuya – Dr Aliyu U. Tilde

Daga ina zan dauki mataimakina? Wannan ita ce damuwar Bola Ahmed Tinubu, dantakarar shugaban kasa a APC, a yanzu.Dr Aliyu U.Tilde ya rahoto a shafinsa

Ba kamar Atiku na PDP ba, wanda kai tsaye ya san daga kudancin Nijeriya zai dauko nasa, kuma Kirista, walau daga cikin Inyamurai ko daga y’an Neja Delta.

Shi Tinubu yana tsaka mai wuya. A Arewa wa zai dauka? Musulmi ko kirista?

Mutanensa Kirista irin su Babachir Lawal sun ce in ya dauki Musulmi tabbas ba zai ci zabe ba, saboda Kiristoci za su gwammace zabar Atiku wanda yake da Kirista mataimaki.

A daya bangaren, idan Tinubu ya dauki Kirista, to Musulmi yan’arewa wadanda su ne wadanda suka fi yawa a Arewa za su ga cewa an mai da su tsiraru, yankallo, abunda ba a taba yi ba a mulkin Nijeriya. Haka zai sa su runtuma wajen Atiku.

Da alama dai duk inda Tinubu ya yi, Atiku zai ce gaba ta kai shi. Ga shi magudi yana kara wuya. Ga shi ba zaben fid da gwani ba ne na mutane kalilan balle a ce Dola za ta yi aiki. Ga INEC ta matsa ta ce cikin sati guda kowane ya fito da mataimakinsa.

Gaba kura, baya siyaki. Ni Tinubu! Ina zan sa kai na?

In da kai ne Tinubu, ya za ka yi?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button