Kastina : Ƴan bindiga sun yi shigar mata sanye da hijabai, sun kai hari a ofishin ƴan sanda


Ƴan bindiga sun yi shigar mata sanye da hijabai, sun kai hari a ofishin ƴan sanda, sun kashe Jami’i ɗaya a jihar Katsina
Wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi sun kai hari ofishin ‘yansanda, tare da kashe dan sanda guda daya a kauyen Sakijiki da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Aliyu Sadiq, a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wani dan sanda ya samu rauni a harin, ba ya ga wani daya da ya rasu.
A cewar Sadiq, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis, wanda ‘yan bindigar suka shigo garin sanye hijabi, suka farmaki ofishin ‘yansanda da ke kauyen Saki Jiki a Karamar Hukumar Batsari.
Katsina Reporters ta samu cewa, ƴan sandan sun yi artabu da ɓarayin dajin inda suka yi nasarar dakile harin. Sai dai jami’i daya ya rasa ransa sannan wani ya samu rauni sakamakon harin.
Karamar hukumar Batsari dai na fuskantar sabbin hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan. Wanda cikin mako guda, ‘yan bindiga sun kai hari biyu a yankin.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



