Shugaba Buhari Yayi Alla-wadai Da Kai Hari Makarantar Kwana A Kankara
Daga Buhari Sallau
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Asabar yayi kak-kausan Alla-wadai da harin ‘yan fashi a Makarantar Sakandaren Kimiyya na Gwamnati dake Kankara a jihar Katsina, ya tuhumi Soji da ‘yan Sanda da subi sawun maharan don Tabbatar da ba’asamu wani Dalibi daya bata ko yaji rauni ba.
Shugaban ya bukaci Mahukuntan makarantar dasu fito da binciken yawan Daliban, biyo bayan harbe harbe a ciki da wajen Makarantar wanda yasa Daruruwan Daliban arcewa cikin rudani da haye shingen makaranta. Iyaye da nan take suka garzaya makarantar da Cire ‘ya’yan su da masu kula dasu ana bukatar su Sanar da Makaranta da Jami’an ‘yan sanda domin samun cikakkiyar dama don gane yawan ‘yan makarantar.
“Nayi Alla-wadai matuka kan harin tsoro na ‘yan fashi akan yaran Makarantar kwana na Kimiyya a Kankara da basuji ba basu gani ba. Addu’ar mu na tare da Iyalai Daliban, Shugaba Buhari ya fadi haka a yayin dayayi Alkawarin cigaba da Mara baya wa ‘yan sanda da Soji a gwagwarmayan yaki da ‘yan Ta’adda da ‘yan fashi da bindiga.
A Cikin jawabi da Shugaban ya samu na baya bayan nan daga Gwamna Aminu Bello Masari, Wanda tun tuni yana tattunawa dashi da Shugaban Hafsan Sojojin Najeriya Jeneral Tukur Burutai, tuni Sojoji bayan samun talllafi sun gano mafakar Barayin da suke da mafaka a Dajin Zango/Paula a Garin Kankara an samu harbe harben bindiga tsakanin a yayin gudanar da aikin kawo yanzu ‘yan sanda sun ce babu wani labarin rasa ‘yan makaranta ko dalibi guda.
Shugaban kasa ya Umarci akara tura Jami’an tsaro ga dukkan Makarantu wanda haka yayi dai dai da shirin Gwamnati na Kare Makaranto.
Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a


