Labarai

Datti Assalafiy yayiwa Dr. Sheriff Almuhajir martani mai zafi akan Kirifto

A yan kwanakin baya Dafta sheriff Almuhajir yayi magana akan sakarici da yauta da yake gani matasan mu suke yi akan harka kasuwancin yanar gizo kirifto kenan wanda hakan ya sanya sunkayi masa tirere.

Shine yau ma Dr. Sheriff Almuhajir ya sake zuwa da karin bayyani irin ganin rashin tunani da matasa ke yi a harka mining, wanda a yanzu itace hanya mafi sauki baka da ko sisi ka samu kuɗi a harka internet.

Yau sheriff ya sake wallafa wani rubutu a shafinsa na facebook wanda shine yayi sanadiyar datti Assalafiy yayi masa martani mai zafi akan maganarsa.

Ga abinda ya rubuta.

Jama’ah babu wanda yace muku ba’a samun kudi a crypto ko minning koma menene, abunda aka ce muku shine kudin banza ne da ake samun su da jarin banza, kuma kowa ya sani banza daga karshe ita ke jawo hasarar banza. Mutane ne suke muku wayo, su sutale dukiyar yan’uwan ku, su baku, daga baya su sutale ta wawayen cikin ku su tattara su karfafa dukiyar su da shi.

In banda karancin tunani ta yaya za ka kama minning ba ka saka ko sisi ba kuma a baka daloli sai ka yi tsammani ka samu sana’ah, sana’ar me, tayaya me ka sayar ko me aka saya a wajen ka? Yadda kuke cewa kun ci riba babu ko sisi, haka wasun ku suke cewa an sutale musu kudade, da kuna da wayo da kun gane cewa kudin su ne aka kwashe aka baku kadan aka handame sauran.

Ni ban ga ta yadda za’a yi a yaudare ni da wannan sana’ar ba, ba yadda zan yi in baka sisi na sai na ga abunda kake saya ko kake sayarwa.”.

Ga martanin da Datti Assalafiy yayi masa a shafinsa na facebook shima.

“IKON ALLAH

Wai fa wanda yake wannan maganar yana da Digiri na uku a bangaren harkokin kasuwanci da bankuna na Musulunci

Ya kamata kuwa ace ya dan san wani abu dangane da abinda ake kira da Connected Economy, tunda dai ya nuna bai san komai akan Blockchain da Cryptocurrency ba

Misali, mutumin da zai dauki diga bai kashe sisin kobo ba ya tafi jeji ya fara tonon ma’adinai har ya tono zinare ya je ya sayar, haka abin yake garemu ‘yan Crypto wadanda muke mining tokens ko coins a yanar gizo

Kuma ma “mining” ake cewa ba “minning” ba kamar yadda ka rubuta, kalma ce na Turanci, kaga tun anan a rubutunka ka kwafsa, baka san ma abinda mukeyi ba

Mutane sun yarda zinare abune mai daraja, shiyasa ake tononsa ake sayarwa, to haka mutane a karkashin Connected Economy suka yarda da Cryptocurrency a matsayin abune mai daraja da ake saye da sayarwa da shi

Don Allah Dr ka rufawa kanka asiri kana manajan Banki guda amma baka san Connected Economy ba? Dole a sa maka alamar tambaya cewa a ina kayi karatun Digiri?

Kaga zaka cigaba da zubar da kima da mutuncin jiharka na Yobe, shiyasa wasu ma suke maka habaici da cewa Mai digirin ‘yan Kotono

Dr je ka nemi wata Lecture da uban ‘yan ICT a Nigeria Marigayi Sheikh Albaniy Zaria yayi mai taken INTERNET BAIWAR ALLAH, Insha Allah zaka fita daga cikin rudun da kake ciki akan ‘yan Crypto”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button