Hukuncin Pre-order A musulunci – sheikh Aminu Daurawa


Wannan wani karatu ne akan masu hada hadar kasuwancin ta yanar gizon “Online business” wato Pre-order shine a takaici ka ka saye abu alhalin babu shi a hannu ko a shago.
Kudin da ka bayar da shi za’a yi amfani aje a sayo wancan kaya sai mutum ya cire ribar sa sai ya ai koma ka kayan da ka saye to wannan haramu ne a musulunci.
A cikin wani faifan bidiyo ash sheikh Aminu Ibrahim daurawa yayi bayyani kwata filla da aka dora a shin Wa’azi da fadakarwa a shafin tiktok
“Misali idan kana da shago kaje wajen katin yaddi ka dauko bashi a rubuta kaga idan ka sayar kuɗi za’a mayar.
Amma abinda Shari’a bata halla ta muku shi ba,har abada baza mu hallata muku ba, shine ka karbi kudin mutum babu abu daga baya kaje ka sayo , ba wanda zai hallata wannan indai yana tsoron Allah– inji sheikh daurawa
Malam ya ƙara bayar da misali da mutane zasu fahimci irin kasuwanci da malam yake magana.
” Kamar inzo in saya maka wannan kofi a shafina ina da kofi wannan kalar ₦500 dari biyar kuma babu hoto kawai naje na dauka , sai wani yace malam inason biyar,malam inason goma, wani yace ina son ashiri, sai na basu akawun numba su sanya kuɗi sai bayan kun tura naje kasuwa bayan na sayar na karbi kudi sai in tafi nema.
Sai ankayi rashin Sa’a wani yaje ya saye, ni kuma nan na sayar muku, yanzu dole sai na ɓukaci nayi muku karya.
Na biyu zan iya sayarwa da mutane akan naira dari dari ₦100, Ni kuma nasan saba’in ake sayar da shi , na sayar muku da Naira ɗari , ashe ban sani ba a lokacin da nake sayar da shi Naira dari ya tashi ya koma Naira dari da hamsin ₦150. Bayan na karbi kudin mutane har riba naje saye ya tashi yah zanyi kenan?
Kaga a Shari’a nan dole in nema hamsin, hamsin din nan in sayo akan ₦150 su kuma in sayar musu akan naira dari dari saboda a haka munkayi chiniki, kaga na fadi hamsin hamsin.
To shi dan kayi – nayi kwata kwata baya son asara, saboda bashi da kudi ba da wuri bashi da rumfa baya da jari saboda shi ya shiga tsakanin mai saye da mai sayarwa amma duka ba chinikin gaskiya yake ba , kunga wannan zaice hala ne” – inji Daurawa.
Ga bidiyon nan.
@waazi_da_fadakarwa Pre order “placing an order for an item before it is available for purchase”. Pre order “shine ka bada kudin abu alhalin kuma babu abun a shago kuma babu abun a hannu. kudin daka bayar dashi za ayi amfani aje a siyo kayan, shi wanda ya siyo ya cire riban sa sannan ya kawo ma kayan. Wannan abu haramun ne❌ #waazi_da_fadakarwa #waazihaussa #kano #arewa #arewa__tiktok #malamai #sunnah #hausa #hausatiktok #muslim #daurawa #malamaminudaurawa #isaalipantami #nigeria #waazin_hausa #fadakarwa #allah #allahuakbar #hausawa #addua #deen #dua #waazin_hausa #waazitiktokhaussa ♬ original sound – Wa’azi Da Fadakarwa⭐️





