Labarai

Mai katanga ya zo matsayin na ukku A Gasar daukar hoto ta Afrika-china na 2023

Advertisment

Gogaggen mai daukar hoto daga yankin Arewacin Nijeriya, Sani Muhammad Maikatanga, ya taki matsayi na uku a gasar da Cibiyar Africa China Journalist ta shirya na 2023 kwanan nan.

Masu sana’ar daukar hoto daga sassan Afrika ne suka shiga gasar inda kowannensu ya baje fasaharsa

Jaridar Blueprint na ruwaito Bayan lura da kuma darje ayyukan da aka gabatar musu, a karshe alkalan gasar sun ayyana Sani Maikatanga daga Nijeriya a matsayin wanda ya zo na uku.

Mai katanga ya zo matsayin na ukku A Gasar daukar hoto ta Afrika-china na 2023
Mai katanga ya zo matsayin na ukku A Gasar daukar hoto ta Afrika-china na 2023

Hoton da ya kai Sani wannan matsayi ya nuna dangantakar al’adu ne tsakanin Afirka da Chaina wanda ya dauki hankali malarta gasar.

A hirarsa da manema labarai, Sani Muhammad Maikatanga, ya nuna farin cikinsa da hotonsa ya samu karbuwa a wannan gasa, tare da bayyana irin muhimmancin da hoto ke da shi a fagen sadarwa.

Cibiyar Africa China Journalist Forum ta yaba wa Maikatanga bisa kokari da kwarewarsa game da ayyuakansa.

A cewar cibiyar, nasarar da Maikatanga ke samu a harkokinsa cigaba ne ga Nijeriya da ma Afirka baki daya.

Ndvolu daga Afirka ta Kudu shi ne wanda ya zo na daya a gasar, sai kuma Ihsaan Haffejee shi ma daga Afirka ta Kudu, ya zo na biyu.

~Blueprint

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button