Labarai

Abuja ta Zama Birni Mafi Ban tsoro a Duniya – Bulama Bukarti

Advertisment

Wani masani kan harkokin tsaro, Bulama Bukarti, yace Abuja ta zama daya daga cikin biranen da suka fi firgita a Duniya, Inda a baya-bayan nan ake fama da matsalar sace-sacen mutane da fashi da makami da sauran miyagun ayyuka.

Bukarti ya bayyana hakan ne a wata hira da Gidan Talabijin na Channels TV’s Siyasa a jiya Litinin.

Yace, “A manyan mahadara dake Abuja, masu laifi da ‘yan fashi da makami da ke yin kame-kame a matsayin direbobin tasi suna yi wa ‘yan Nijeriya fashi da makami ta hanyar da ba mu taɓa Gani ba.

Ya ƙara da cewa, “Abuja na zama ɗaya daga cikin manyan biranen birnin tarayya mafi firgita a duniya.”

Abuja ta Zama Birni Mafi Ban tsoro a Duniya - Bulama Bukarti
Abuja ta Zama Birni Mafi Ban tsoro a Duniya – Bulama Bukarti

Bukarti yace abin dake faruwa a Abuja na nuni da irin abubuwan da ke faruwa a fadin Najeriya.

Yace, “Sama da Mutane Dubu 9,700 aka kashe a Shekarar da ta Gabata a 2023 a faɗin Najeriya. Abuja ba za ta tsira daga hakan ba, Domin muddin ka bar rashin tsaro ya yi ta’azzara a fadin Nijeriya, to za ta samu hanyar Abuja.”

A cewar Bukarti, Bayanan sirri sun nuna cewa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu tayar da ƙayar baya Daga shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiyar geopolitical sun shiga Abuja yayin da wasu ke Gudanar da ayyukansu daga jihohin kan iyaka kamar Kogi da Kaduna da Neja da kuma Nasarawa.

“Sama da Mutane 200 ne aka kashe ko kuma aka sace a Abuja a cikin watanni ukun da suka Gabata na Shekarar 2023,” inji masanin, Inda ya bayyana cewa wannan mummunar dabi’ar zata kori masu zuba jari da kuma hana jami’an diflomasiyya zama a babban birnin ƙasar.

Bukarti ya Buƙaci jami’an tsaro dasu dauki matakin tsaro a Abuja da sauran sassan ƙasar nan.

“Hanyar tsaron Abuja itace a kai farmaki ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasar nan,” inji shi.

Idan ba a manta ba a baya-bayan nan an samu labarin sace wasu ‘yan uwa shida da mahaifinsu a ƙaramar Hukumar Bwari dake Abuja a Ranar 3 ga watan Janairun 2024.

Masu Garkuwa da mutanen sun kashe ɗaya Daga cikin ‘yan uwa mata mai suna Nabeehah bayan da iyayensu suka kasa cika wa’adin biyan kudin fansa Naira Miliyan 60.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button