Labarai

Abin a yaba : Buhari ya gwangwajewa wani masoyinsa da mota da buhun Shinkafa biyar

Advertisment

Wani masoyin buhari kuma dattijo ya samu ziyarar toshon shugaban kasa Muhammadu buhari a garin daura inda ya samu goma ta arziki, inda tsohon shugaban kasar Muhammadu buhari ya gwangwajewa dattijo da mota da shinkafa domin yaje ya yayi liyafa shida iyalinsa kamar yadda tsohon mai taimaka wa Muhammadu buhari a kafafen sada zumunta Buhari sallau a shafinsa na sada zumunta.

A Jiya Asabar Wadda Tayi dai dai da 6/01/2024. Wani tsoho ya Samu Damar Ziyartar Tsohon Shugaban Kasa general Muhammadu buhari, a gidansa dake daura.

Ziyarar Tasamo Asali Ne Domin Kai Masa Wani Cikakken Masoyinsa Na Garin Yashe Wanda Aka Fi Sani Da Suna, (sai baba buhari) Ko Kuma (harunanmu), Hakika Tsohon Shugaban Kasa Yaji Dadi Da Kuma Nuna Farin Cikinsa Akan Wannan Masoyin Nasa Domin Yaji Duk Irin Soyayyar Da Yake Masa Da Kuma Hidima Da Yake Akansa.

Mai girma tsohon shugaban kasa ya Gwangwaje Dattijon Da Sabuwar Mota kirar GOLF 3, Da Kuma Buhun Shinkafa 5, Da Kuma Wasu Kudade.

Hausaloaded ya samu tattara martanin mutane a karashin wannan rubutu suna cewa.

@Hussaini s Maigana ga abinda yake cewa:

Suma mutane da jarabarsu ,mutuminnan yace baya so a rinqa ziyartarsa .
Amma saboda rashin zuciya nawasunmu Sai sunje.

Kar a manta fa har alkaba’i yake Neman jawo Mana saboda masu ziyartarsa.

@Abubakar sadeeq tajadden yana cewa :

Wallahi kullum burina Allah ya nuna man ranan da zanyi ido biyu da general muhammadu buhari. Allah ya qarawa baba buhari lafiya, da nisan kwana
Allah ya tsare Mana gabanshi da bayanshi alfarmar fiyayyen halitta muhammurrasulillah SAW.

@saifullahee Ibn sallau yana mai cewa :

Wato Baba Dai Har Yanxu Yana Nan Akan Bakar Shi Baya Son Cima Zaune, Shiyasa Ya Gwangwaje Dattijo Da Golf 3 Don Ya Dunga Fita Neman Na Magi, Allah Ya Saka Da Alkhairy Baba Manjo.

@Ibrahim Alhaji shehu cewa yake ;

Yawwa, haka akeyiwa masoyi, Amma mutane sana ta nuna soyayyar su gareka Amma baba sai kayi burus dasu, idan anyi magana kace Kai bakasata,to baba kasani tunda har kazama shugaban kasa agurun wasu fa kayi Sata duk da dai mu Muna da kyakykyawan zaton bakayiba. Kuma duk abun daka ba masoyinka baka biyashiba.muna Maka fatan alkhairi.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button