Labarai

Har yanzu babu dattijon da ke son talakan Nijeriya kamar Buhari – sani zangina

Kamar kullum jaridar Dclhausa hausa ta samu tattaunawa da wani masoyin tsohon shugaban kasa Muhammadu buhari tare da mai gabatarwa a cikin tattaunawar Abdullahi Garba, inda za’a tattaunawa da shi cmrd sani Ahmad zangina akan wasu kalamai da buhari yayi yan kwana kwanan nan kan cewa ‘ yayi murna da Tinubu ya ƙara farashin man fetur’ wanda maganar farkon fitowarta ake kallon karya ce ake yiwa tsohon shugaban kasa Muhammadu buhari, to shine sani ahmad zangina ya fito zaiyi fashin baki akan waɗannan kalamai na buhari.

A cikin tattaunawar da sunkayi da Dclhausa ta fara yi masa tambaya akan wasu kalamai da tsohon shugaban kasar Muhammadu buhari yayi a wani taro na masu ta’amali da miyagun kwayoyi a jihar Katsina.

Kamar dai yadda kowa yaji wasu kalamai na baba buhari yan kwana kin nan wanda sun tada hazo matuƙa, inaga abu ne kawai na rashin fahimta ko rashin adalci akan shi tsohon shugaban kasar Muhammadu buhari zaka sha mamaki ni a matsayina ina daukar waliyi a siyasar Nijeriya.

Har yanzu babu wanda ya kawo mana aƙala ace ya kai za’a kwatantan shi da Muhammadu buhari koda a mataki ne na ukku ko yayi kafaɗa kafaɗa da shi ba domin banganshi ba kuma ba’a nuna min shi ba, ba ƙalubalanci duk wanda yace naya da ja ya kawo nashi gwani a dora shi a faifa muyi mai tsifa, muga yadda zata kaya.

To kalamai na buhari a tawa fahimta ne akan dai-dai yana ƙoƙarin mutuncinsa da ƙimarsa da yan Nijeriya suke da shi, idan na auna tun daga lokacin da anka fara siyasa dimokuraɗiyya tun daga lokacin Olusegun Obasanjo da yayi shekara takwas zuwa yau babu wanda ya kamala mulkinsa yake samun mutane suna zuwa gidansa kamar shi na Muhammadu buhari suna gaishe shi suna taya shi murna.

Yadda mutane suke tururuwa zuwa gidansa da anka ƙara kuɗin man fetur a tunaninsa kila wannan wata dama ce da talakawa zasu daina zuwa gidansa zasu rage tururuwa amma sai yaga abun ya canza salo domin sai mutane suke haduwa suyi tashar moto suje gaishe shi wannan shine kawai fahimta ta abinda yake so ya bayyana.

Wannan sheri ne na yan adawa masu son suga an ɓata masa suna – inji zangina.

Ga bidiyon nan

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button