Labarai

Ƴan kirifto sunyiwa Dr. Sherrif almuhajir tumu tumu akan maganar sa

Advertisment

Dr.sheriff almuhajir yayi wata magana a shafinsa na facebook akan matasa masana harka yanar gizo da suke hada hadar kasuwancin yanar gizo kirifto kenan inda kafin kace kobo sunyi masa dirar mikiya da masa martani.

Matasan yanar gizo sun bayyana dafta a matsayin tabbas shi jahili ne da yake da digiri ukku amma yana magana irin ta wadda bai shiga aji ba.

Ga maganar tasa.

Anan Arewa dai sana’ar crypto ta janyo yara matasa da dama sun salwantar da dukiyar iyayen su wanda ba’a ba su ba, ko su yi dubarun dauke dukiyar su jefa ta kuma ta hallaka a ciki, hakanan wasu sun yi kuka saboda hasarar dukiya da suka yi.

Advertisment

Yanzu farkon sabuwar shekara ce, kamfanunnukan crypto sun kara fitowa suna yaudarar matasa suna jefa musu kudade a asusun su da sunan riba, saboda daga baya su Jane kudaden kuma a sake dawowa ana ta maganar an salube kudaden su an yi hasara.

Ƴan kirifto sunyiwa Dr. Sherrif almuhajir tumu tumu akan maganar sa
Ƴan kirifto sunyiwa Dr. Sherrif almuhajir tumu tumu akan maganar sa

Ina kira ga iyaye da ma su fada aji, da su yi kokarin sa ido akan abunda ya’yan su ke yi a wayoyin su, domin ina tsoron kar a koyawa yaran mu data, ko a kashe musu zuciyar nema, ko ma daga karshe a zaftare kudaden su su kasa hakuri su koma shaye-shaye.

Amma fa wannan shawara ce na bayar kawai, saboda na san da yawan mutane da suka yi hasara akan wannan sana’ar, kuma yanzu haka akwai matashin da ya ke fursuna sakamakon wannan sana’ar.”

Hausaloaded ta tattaro kadan daga cikin mutanen da sunkayi masa martani

 

@Datti Assalafiy cewa yake :

Dr da hakuri kayi da maganar Crypto da ka rufawa kanka asiri, saboda gaskiya baka san komai game da crypto ba, da zaran kayi maganar sai rashin saninka ya kara bayyana a fili.
Crypto ilmi ne mai zaman kansa, ka je ka nema

@Adam Muhammad mukhtar ga abinda yake cewa:

You’re nothing but an educated-illiterate of Blockchain and Cryptocurrencies.

A dage da neman ilimi akan abu kafin kace uffan akai. Ita Crypto in kayi magana akan ta baka san komai ba, jahilcinka akaine zai baiyana.

@Hafsat Ermum cewa take :

Dr Dan Allah Ka Daina Irin Wannnan Maganan,Mu Yan Baiwa Bamu Cika Son Irinku da kuke da Kima a idon Jama’a kuna magana Kara Zube Ba,Yakamata Dukkan Abinda Zakai Magana akai Kayi Bincike Yanda Ya kamata….

Akwai Banbanci Tsakanin Ilimin Boko Da ilimin Crypto….

Dan Allah Ka daina jawo Abinda yara Zasuzo suna maka Rashin kunya.

@Deen yashe Dabai yana mai baiwa dafta shawara cewa :

Dakta kamata ya yi ace ka yi shiru gaskiya. Dalili kuwa shi ne ba ka da masaniya a wannan fannin.

@muhammad abdulrahman yana cewa :

Dr wallahi ina mamakin makarantar data dauki shaidar karatu ta baka, simple binkice bazaka iya ba. Abinda baka fahimta ba, dan fa kawai kana Dr hakan bazai sa ka fahimci Crypto ba.

A aikin banza gashi nan yara yan secondary school da suka fahimci yadda crypto yake sai dariya suke ma, kaga wannan ai wulakanta ilimi ne. A ce Dr guda yara yan primary suna masa dariya saboda sun fuskanci jahililci da rashin fahimtar komai, da ma rashin iya binkice.

Abinda kuke dauka shine: Ai dan kawai ku Dr ne, to kuna da bakin magana akan crypto. Ko kuma tsofaffin ma’aikatan banki. Wallahi cikin dalibai na dana koyar a crypto a dauki matsayi na rayuwa da kuma gogewa, Allah ba abinda basu fika ba. Baka san crypto ba maigidana, kazo ka zauna a aji a koya maka ka gane banbanci crypto da abinda kake magana akai.

Cikin last year crypto ɗin da ka jahilta aka halatta ta, sannan a ciki aka dauki wani Company mai suna Convecsity zaiyiwa Nigeria Coin nata na kanta. Shiyasa inaga akwai buƙatar ka fahimci menene crypto ɗin. Kasuwar crypto da kake magana tana darajar $1.7Trillion, kimanin Naira Trillion dubu biyu, da Trillion 145. Ko muce Naira Quadrillion 2 da Trillion 145 kenan.

Wallahi baka san komai ba a crypto, idan kuma kana jin kasan wani abu. Toh dan Allah ka haɗa live ni da kai mu tattauna. Wai a haka ma naga kamar bangaren abinda ya shafi Finance kake yi, kaga idan haka ne yakamata kasan menene Cryptocurrency da Blockchain koda a definition ne.

“Kar a manta ranar 19 ga watan nan za’a yi launching ICE a OKX” .

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button