Labarai

Yan sanda sun biya wani matashi tarar miliyan Uku 3 sakamakon cin zarafin sa da sunkai

A yau din nan an kai karshen Shari’a wani matashi mai sunan dayyabu auwalu matukin adaidaita sahu da wasu yan sanda naci zarafinsa inda nan take ya samu yanci kuma anka biyashi makudan kudin kamar yadda Barrister Abba hakimi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Dayyabu Auwalu matukin Adaidaita Sahu ya zama miloniya

Bayan cin tarar hukumar dauka da ladabtar da yan sanda (Police Service Commission )da babbar kotun tarayya (Federal High Court)tayi, Dayyabu ya karbi cekin kudi na Naira Miliyan 3 wanda kotu tace a cira daga asusun bankin hukumar a bashi diyya sakamakon cin zarafin sa da aka yi.

Yan sanda sun biya wani matashi tarar miliyan Uku 3 sakamakon cin zarafin sa da sunkai
Dayyabu Auwalu

Yan sandan da aka kama da laifi sun hada da Abdullahi Daura, Khalifa da kuma tsohon DPOn Kuntau Police Station Kano wato CSP Abdulhadi.

Da fatan wannan zai zama jan kunne ga yan sanda masu cin zarafin al’umma da ma ita kanta hukumar dauka da ladabtar da yan sanda din.

Alhamdulillah!”.

Shine jaridaradio na zanta da Barrister abba hakimi inda yayi musu karin bayyanin cikin sautin Murya gashi nan ku saurara kuji.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button